Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce idan Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zaɓen 2027, gwamnatinsa za ta zama ta haɗin kai, kamar yadda kwamitin yaƙin neman zaɓensa ya ƙunshi ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban.

Akpabio ya bayyana hakan ne a zaman majalisar dattawa ranar Laraba, yayin da yake mayar da martani kan jawabin shugaban masu rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele, game da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.

Ya bayyana haɗa ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa cikin kwamitin a matsayin wani sabon salo a siyasar Najeriya tun bayan komawa mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Akpabio ya taya Tinubu, da shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da shugabannin jam’iyyun da suka shiga kwamitin murna.

Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo na APGA, da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke na Accord Party, da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike na PDP, bisa shiga kwamitin.

Ya ce shiga kwamitin da waɗannan ’yan siyasa suka yi na nuna cewa iya aiki da gudummawar mutum ba lallai ne su dogara da jam’iyyar da yake ciki ba.

Tun da farko, Bamidele ya bayyana cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen ya haɗa shugabanni daga jam’iyyu daban-daban, inda Soludo da Adeleke za su kasance masu kula da yaƙin neman zaɓen a jihohinsu, yayin da Wike zai jagoranci ayyukan yaƙin neman zaɓen a Abuja.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro, na PDP mai wakiltar Benue ta Kudu, ya goyi bayan kudirin dage zaman majalisar zuwa ranar Alhamis.

Bamidele ya ce yana fatan yaƙin neman zaɓen zai mayar da hankali kan muhawarar manufofi da ƙarfafa dimokuraɗiyyar Najeriya.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *