An bayyana haɗin gwiwar ne a gefen taron rana ta uku ta taron shekara-shekara na Alliance for Hydromet Development, wanda aka gudanar a Legas, Najeriya.
Shirin na da manufar samar wa manoma da bayanan yanayi masu sauƙin fahimta kuma a kan lokaci, domin taimaka musu wajen tsara ayyukan noma da yanke shawarar da ta dace.
- Majalisar Dattawa ta amince da kafa kwalejin aikin gona a Shani
- Wike ya buƙaci a sauya siyasar neman gata zuwa siyasar ɗaukar nauyi
- Masari ya buƙaci matan ’yan majalisa su ƙara wayar da kan jama’a gabanin zaɓen 2027
Darakta-Janar kuma Babban Jami’in Gudanarwa na NiMet, Farfesa Charles Anosike, ya jaddada muhimmancin daidaita bayanan yanayi da ake samarwa ga masu ruwa da tsaki a dukkan matakan harkokin noma.
Ya ce dole ne haɗin gwiwar ya kasance mai samar da sakamako tare da kawo alfanu kai tsaye ga manoma.
A nasa jawabin, Babban Jami’in Gudanarwa na TomorrowNow, Brian Miranda, ya tabbatar wa shugabannin NiMet cewa ƙungiyarsa za ta himmatu wajen samar da ayyukan bayar da shawarwarin yanayi ga sassan noma da kiwon dabbobi a faɗin Najeriya.
Ana sa ran haɗin gwiwar zai inganta damar manoma da masu kiwon dabbobi na samun bayanan yanayi da shawarwarin da za su taimaka musu wajen yanke shawara mai kyau da kuma ƙara jure sauye-sauyen yanayi a harkokin noma.