Masari ya yi wannan kira ne yayin da ya karɓi wata tawagar ƙungiyar a ofishinsa da ke Asokoro, Abuja, ranar 15 ga Oktoba, 2026.
Tawagar ta samu jagorancin shugabar ƙungiyar, Hajiya Yasmin Dahiru Dawaki.
- Yadda za ka tantance amincewar NCC kafin sayen waya a Najeriya
- Majalisar Dattawa ta amince da kafa kwalejin aikin gona a Shani
A yayin ganawar, Masari ya buƙaci mambobin ƙungiyar su ƙara hulɗa da al’ummomin da suke wakilta, inganta ƙarfafa mata da kuma yaɗa nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce ta samu.
Ya kuma buƙaci su wayar da kan jama’a domin samun goyon bayan sake zaɓen Tinubu a 2027, tare da kira ga masu zaɓe da su zaɓi ’yan takarar APC daga sama har ƙasa.
Masari ya bayyana rawar da mata za su taka wajen samun nasarar zaɓe ta hanyar wayar da kan jama’a da tattara goyon baya a matakin al’umma.
Shi ma mai kula da shirin NEPAD, Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, ya buƙaci mambobin ƙungiyar su kasance masu haɗin kai, gudanar da ayyukansu yadda ya kamata da kuma ƙarfafa hulɗarsu da jama’a a matakin ƙasa.
Sauran waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Farfesa Muhammad Kabir Isa, shugaban ma’aikatan mai ba shugaban ƙasa shawara, da Malam Yahaya Bello, mai ba Ibrahim Kabir Masari shawara kan matasa da harkokin kasuwanci.