Kwamandan Rundunar Sojin Saman da ke kula da ayyukan musamman, Air Vice Marshal MC Ekwueme, ne ya kai ziyarar bisa umarnin Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke.
A yayin ganawar, ya amince da damuwar al’ummar, tare da tabbatar musu cewa rundunar za ta yi aiki don magance matsalolin da aka gabatar.
Rundunar ta bayyana cewa ana samun ci gaba a aikin gano tarkacen jirgin, duk da wahalar yanayin wurin da kuma ƙalubalen da ake fuskanta a ƙarƙashin ruwa.
- NiMet da TomorrowNow sun haɗa kai don inganta hasashen yanayi ga manoman Najeriya
- Masari ya buƙaci matan ’yan majalisa su ƙara wayar da kan jama’a gabanin zaɓen 2027
- Wike ya buƙaci a sauya siyasar neman gata zuwa siyasar ɗaukar nauyi
An tura injinan fitar da ruwa da dama domin rage ruwan da ke kewaye da wurin da jirgin ya faɗa, matakin da ake buƙata kafin a iya isa ga babban tarkacen jirgin da har yanzu yake ƙarƙashin ruwa, kuma ya nutse sosai a gadon kogin.
Ta ce aikin na buƙatar ƙoƙari mai ɗorewa, ƙwararrun ma’aikata da kayan aiki na musamman, tare da kyakkyawan tsarin haɗin gwiwa domin gudanar da aikin cikin aminci.
Babban Hafsan Sojin Saman ya kuma sake tabbatar da cewa rundunar za ta tallafa wa iyalan mamatan a wannan lokaci mai wahala. Tallafin zai haɗa da haƙƙoƙin da doka ta tanada, kuɗaɗen tallafi na musamman, guraben karatu ga yaran da suka cancanta da sauran alawus-alawus na jin daɗi da aka amince da su.
Rundunar ta ƙara da cewa tana ci gaba da hulɗa da iyalan waɗanda abin ya shafa, kuma ta samar da layin waya na musamman a hedikwatarta domin sauƙaƙa musu samun sahihan bayanai.
Ta kuma tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tattaunawa da al’ummar Igbokoda kan matsalolin muhalli, tare da sanar da jama’a sahihan bayanai yayin da aikin gano tarkacen jirgin ke ci gaba.