An shiga tashin hankali a filin jirgin saman Abuja a ranar Alhamis, bayan da kofar wani jirgin sama kirar CL60 mallakin kamfanin Triton Aviation  ta bude a sararin samaniya, jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Jirgin mai lambar rajista T7-SEI da lambar tashi DWC052, yana kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas lokacin da lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:20 na yamma.

Rahotanni sun  nuna cewa ma’aikatan jirgin sun sanar da hasumiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama cewa ƙofar jirgin ta buɗe a lokacin da yake shawagi a sararin samaniya.

Wannan ya sa jami’in kula da radar da ke lura da saukar jiragen sama ya umarci jirgin da ya koma Abuja domin saukar gaggawa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu damar jin ta bakin kamfanin Triton Aviation, wanda ke gudanar da zirga-zirgar jirgin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *