Sabon Shugaban Hukumar Ƙwallon Kwando ta Najeriya (NBBF) Dr. Mustapha Abdullahi ya yi alƙawarin kawo sauyi a wasan ƙwallon kwando a Najeriya ta hanyar kawo gyare-gyare a hukumance, da cigaban matasa a matakin farko, da inganta jin daɗin ’yan wasa, da kuma ƙulla kyakkyawan haɗin gwiwa na kasuwanci.
Dr Abdullahi ya bayyana hakan ne bayan rantsar da shi da aka yi a matsayin Shugaban Hukumar Ƙwallon Kwando ta Najeriya (NBBF).
A jawabinsa na karɓar mulki, sabon shugaban da aka zaba ya nuna godiyarsa ga wakilan da suka dora masa wannan nauyi, inda ya bayyana nasararsa a matsayin wata nasara ce ta haɗin gwiwa ga ’yan wasa, da masu horarwa, da jami’ai, da kuma matasan Najeriya da ke son gina rayuwarsu ta fuskar wasan ƙwallon kwando.
A yayin zaɓen, Abdullahi ya samu ƙuri’u 40, inda ya doke tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar D’Tigers, Olumide Oyedeji wanda ya samu kuri’u takwas.
-
Burkina Faso ta ƙaddamar da gasar ƙwallon ƙafa ta ‘Sovereignty League’
-
Rwanda ta samu yarjejeniyar shekaru 10 ta dawo da gasar Formula One Afirka
-
Dangote Cement za ta shirya gasar ƙwallon ƙafa domin haɗa kan al’ummomi
Ya kuma yi alƙawarin ciyar da wasan ƙwallon kwandon mata gaba tare da neman samun kyakkyawan sakamako a babban tawagar ’yan wasan ƙasar, wato D’Tigers da D’Tigress, gami da ƙungiyoyin matasan ƙasar.
Sabon shugaban na NBBF ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki tukuru domin kafa wani tsari na ƙwallon kwando wanda zai bai wa matasa masu hazaka daga kowane sako da lungu na ƙasar nan kyakkyawan damar wakiltar Najeriya.
Ya ƙara da cewa, ya kamata wasan ƙwallon kwando ya zama wata kafa ta ilimi, da samun aikin yi, da kasuwanci, da kuma hadin kan ƙasa, maimakon kawai ya kasance wasan fafatawa ne kadai.
