Bayan isarsa filin jirgin sama na Ekiti Agro-Allied International Cargo Airport, Shettima ya samu tarba daga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Mataimakinsa, Barau Jibrin, tare da Gwamna Oyebanji da gwamnonin jihohin Kwara, Imo, Sokoto, Kebbi, Ondo da Jigawa.
Sauran manyan baki da suka tarbe shi sun haɗa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; Darakta-Janar na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC, Sanata Abdulaziz Yari; da tsohon Gwamnan Jihar Ondo, Olusegun Mimiko.
- Uzodimma ya jaddada muhimmancin ƙananan hukumomi wajen ci gaban ƙasa
- Kyaftin din Najeriya Rasheedat Ajibade za ta yi jinya tsawon lokaci sakamakon raunin da ta ji a kafarta
- Kwana biyar suka rage kafin taron shugabannin kamfanonin da ke hulɗa da NNPC kan tsaro da lafiya
Za a gudanar da bikin rantsarwar a filin Ekiti Parapo Pavilion da ke Ado-Ekiti, inda Oyebanji da mataimakiyarsa, Monisade Afuye, za su fara wa’adin mulki na biyu na shekaru huɗu.
Rahoton ya bayyana cewa Oyebanji zai zama gwamna na farko a tarihin jihar da ya sake lashe zaɓe domin ci gaba da mulki tun bayan ƙirƙirar jihar a shekarar 1996.
Bikin, mai taken “Ayyukan alheri za su ci gaba”, na zuwa ne bayan Oyebanji ya sake lashe zaɓen gwamna. Ana sa ran sabon wa’adin zai ci gaba da aiwatar da manufofin ci gaban gwamnatinsa.
Shettima ya samu rakiyar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Sule Garo; Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia; Sanata Muntari Dandutse; Ministan Bunƙasa Ma’adinai, Dele Alake; da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Ayyuka na Musamman a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Dakta Aliyu Modibbo Umar, da sauran manyan jami’ai.