Kyaftin din tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya, Rasheedat Ajibade, na fuskantar yiwuwar yin jinyar da za ta dauki tsawon lokaci sakamakon raunin da ta samu a idon sawunta yayin wasan neman gurbin shiga Gasar Olympics da Najeriya ta yi da kasar Comoros.
A cewar rahotanni, za a yiwa yar wasan gaba na Paris Saint-Germain din tiyiya a ranar Jumma’a, 16 ga watar Oktobar, 2026 a kasar Faransa.
Sai dai ba a ambaci ainihin lokacin da za ta dawo filin wasa ba.
-
Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata U17: Flamingos na fatan samun nasara a kan Poland
-
Mustapha Abdullahi ya yi alƙawarin kawo gyare-gyare da cigaban wasan ƙwallon kwando a Najeriya
-
Burkina Faso ta ƙaddamar da gasar ƙwallon ƙafa ta ‘Sovereignty League’
Yar wasan mai shekaru 27 ta samu raunin ne a lokacin wasan zagaye na biyu na neman gurbin shiga Gasar Wasannin Olympics na Los Angeles na 2028, inda Najeriya ta doke Comoros da ci 5-0 a filin wasa na Remo Stars da ke Ikenne, a Jihar Ogun, a ranar Talata.
An fitar da Ajibade daga filin wasa a farkon rabin lokaci sakamakon karo da wata yar wasan Comoros.
Kocin rikon kwarya, Augustine Eguavoen ya bayyana wa manema labarai bayan wasan cewa tawagar likitoci sun tafi da Ajibade domin karin bincike don gano girman raunin da ta samu.
A wancan lokacin, Eguavoen ya ce yana jiran sakamakon binciken likitocin kuma yana fatan raunin ba zai zama mai tsanani ba.
Sai dai daga baya rahotannin da suka fito na cewa ta samu karaya a idon sawunta kuma za a yi mata tiyata.
