Sanarwar hukumar ta ce an gudanar da samamen ne a ranar 15 ga Oktoba, 2026, inda jami’an sashen kula da ƙaura na Barra suka cafke mutane 36 a Barra, yayin da wani haɗin gwiwar jami’an hukumar da rundunar ’yan sandan Intervention Unit ya cafke mutane 79 a Kuyan, da ke gundumar Kiang West.
Haka kuma, jami’an sun cafke wasu mutane 20 a Tanji da kuma 16 a Batokunku, wanda ya kai jimillar waɗanda aka kama zuwa 151.
- Kwanturol Janar na Kwastam ya bukaci sababbin jami’ai su fifita muradun ƙasa
- Dan’iya ya bukaci Tinubu ya sake duba nadin ɗan’uwan gwamnan Sokoto a INEC
Hukumar ta bayyana cewa waɗanda aka cafke sun haɗa da ’yan Senegal, Gambia, Guinea, Mali, Nijar da Saliyo,
Sanarwar ta ce a halin yanzu ana tsare da waɗanda aka cafke a cibiyar riƙe mutane ta hukumar domin gudanar da bincike da sauran matakan da suka dace.
Hukumar Shige da Fice ta Gambia ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa sa ido a kan iyakoki da gudanar da sintiri tare da sauran hukumomin tsaro domin dakile ƙaura ba bisa ƙa’ida ba.
Ta kuma bukaci al’umma, ƙungiyoyin farar hula, kafafen yaɗa labarai da abokan hulɗa na cikin gida da na ƙasashen waje da su ci gaba da ba ta haɗin kai.