Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne bayan ganawa da tawagar CAF ƙarƙashin jagorancin Dakta Christian Emeruwa, wanda ke jagorantar ayyukan shirya bikin kyaututtukan CAF da babban taron hukumar.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar wa tawagar CAF cewa za ta ba da cikakken goyon baya domin ganin an gudanar da bikin cikin nasara.
- Kwankwaso ya ce ba zai janye takararsa ta shugaban ƙasa domin ADC ba
- Hukumar shige da fice ta Gambia ta cafke mutane 35 da ake zargin shirin yin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba
Ya ce za a ba da muhimmanci musamman ga tsaro, harkokin sufuri da sauran kayan aiki, sanya tambari da alamomin bikin, da kuma sauƙaƙa isa wurin da za a gudanar da taron.
Sanwo-Olu ya bayyana Legas a matsayin jiha mai bai wa baiwa, al’adu, kasuwanci da kuzarin matasa muhimmanci.
Ya ce jihar na fatan tarbar shugabannin ƙwallon ƙafa, masu ruwa da tsaki da baƙi daga sassan Afirka da sauran ƙasashen duniya.
Gwamnan ya ƙara da cewa bikin zai ba Legas damar nuna kyakkyawar tarbarta ga baƙi da kuma ƙwarewarta wajen karɓar manyan taruka na ƙasa da ƙasa.