Sanarwar hukumar ta ce jami’an ofishin Mandinaba da sashen sintiri na kan iyaka da ke Tanji ne suka gudanar da samamen daban-daban a ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026.
Hukumar ta bayyana cewa waɗanda aka cafke sun haɗa da ’yan Mali, Guinea, Gambia, Senegal da Ivory Coast.
- ’Yan sandan Kano sun yi alkawarin samar da tsaro mai ƙarfi a zaɓen 2027
- Gwamnatin Sokoto ta ware N10.96bn domin gina hanyoyi 11 a jihar
Sanarwar ta ƙara da cewa cikin waɗanda aka cafke akwai mata huɗu, ciki har da ƙarama wadda ba ta kai shekara 18 ba.
A halin yanzu, ana tsare da waɗanda aka cafke a cibiyar riƙe mutane da ke makarantar horar da jami’an hukumar a Tanji, inda ake tantance su da kuma gudanar da sauran matakan bincike.
Hukumar Shige da Fice ta Gambia ta ce wannan samame na daga cikin ƙoƙarinta na dakile ƙaura ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƙarfafa tsaron iyakokin ƙasar.