Disu ya bayyana hakan ne ranar Asabar, 17 ga Oktoba, 2026, yayin halartar ƙaddamar da littafin Beyond the Bullets: Policing Terrorism in a Democratic System, wanda tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, MD Abubakar, ya rubuta a wani taro da da aka gudanar a Cibiyar Albarkatun ’Yan Sanda da ke Abuja.
A saƙon fatan alherin da ya gabatar a wajen taron, IGP Disu ya ce saƙon littafin ya yi daidai da manufar rundunar, yana mai jaddada cewa ingantaccen aikin ’yan sanda bai taƙaita ga amfani da ƙarfi kawai ba, domin yana buƙatar bin doka, ƙwarewar aiki da amincewar jama’a.
- ADC ta bayyana Atiku a matsayin jagoran da zai iya haɗa kan ’yan Najeriya
- Gwamnatin Sokoto ta ware N10.96bn domin gina hanyoyi 11 a jihar
Ya buƙaci jami’an ’yan sanda da ’yan Najeriya su karanta littafin ba wai kawai domin fahimtar abubuwan da suka faru a baya ba, har ma domin koyon darussan da za su taimaka wajen ci gaba da gyaran rundunar, inganta ƙwarewa da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Ya kuma jaddada cewa yaƙi da ta’addanci dole ne ya kasance cikin tsarin kundin tsarin mulki da mutunta haƙƙin bil’adama.
Disu ya yaba wa MD Abubakar bisa jagorancin da ya bayar a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsalolin tayar da ƙayar baya da ta’addanci, inda ya ce kwarewarsa ta nuna cewa ana iya ɗaukar tsauraran matakai kan masu aikata laifuka ba tare da tauye ƙa’idojin kundin tsarin mulki ba.
Ya bayyana littafin a matsayin muhimmin kayan karatu ga masu tsara manufofi, jami’an tsaro, masana da sauran jama’a, yana mai cewa darussan da ke cikinsa za su taimaka wa shugabannin ’yan sanda na yanzu da na gaba wajen gudanar da ayyukansu a tsarin dimokuraɗiyya.
A madadin jami’ai da sauran ma’aikatan rundunar ’yan sandan Najeriya, IGP Disu ya taya tsohon shugaban rundunar murnar wallafa littafin, tare da yi masa fatan lafiya, tsawon rai da ci gaba da bayar da gudunmawa ga ƙasa.