Mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 18 ga Oktoba, 2026.
Makinde ya yi ikirarin ne yayin taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan kasafin kuɗin shekarar 2027 da aka gudanar a Jami’ar Ibadan ranar Juma’a.
- Hukumar shige da fice ta Gambia ta cafke mutane 35 da ake zargin shirin yin ƙaura ba bisa ƙa’ida ba
- Kwankwaso ya ce ba zai janye takararsa ta shugaban ƙasa domin ADC ba
Gwamnan ya ce jihohi sun riga sun tsara ayyukan raya tattalin arzikinsu da za su gudanar da kuɗin, amma an sanar da su cewa ba za a biya su ba sai bayan zaɓen 2027.
Sai dai Onanuga ya ce idan aka ware naira biliyan 250 ga kowace jiha cikin jihohi 36 na Najeriya, jimillar kuɗin za ta kai naira tiriliyan tara, ba tare da haɗa rabon Gwamnatin Tarayya, da Babban Birnin Tarayya Abuja da ƙananan hukumomi 774 ba.
Ya bayyana cewa bisa tsarin rabon kuɗaɗen Asusun Tarayya, jihohi na samun kashi 26.72 cikin 100 na kuɗaɗen da za a raba.
A cewarsa, domin jihohi su samu naira tiriliyan tara, sai jimillar kuɗin rarar ribar NLNG da aka biya cikin asusun ta zarce naira tiriliyan 33.68, kwatankwacin dala biliyan 25.
Sanarwar ta ce NLNG ba ta taɓa biyan irin wannan adadi na dala biliyan 25 a matsayin raba riba guda ɗaya ba.
Onanuga ya ƙara da cewa kamfanin ya biya Gwamnatin Tarayya kusan dala biliyan 21.5 a matsayin rarar riba cikin shekaru 25, inda ƙasa da dala biliyan uku aka samu tun bayan hawan Shugaba Tinubu mulki.
Onanuga ya bukaci Makinde da ya guji yaɗa bayanan da ya kira na yaudara, yana mai cewa kamata ya yi ya gabatar da hujjoji masu inganci maimakon yin kalaman da ka iya jawo rashin fahimta tsakanin jama’a da Gwamnatin Tarayya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin da fadar shugaban ƙasar ta ce ba su da tushe.