Shirin ya haɗa da tura ɗalibai biyu na Kwalejin Horar da Jami’an Tsaro ta Najeriya (NDA) zuwa Kwalejin Soji ta Rwanda domin yin horo na tsawon shekaru huɗu, tare da samar da damar horo ga ɗaliban sojin Rwanda a Najeriya.
- Sojoji sun kuɓutar da mutane 11 daga hannun masu garkuwa da mutane a Kogi
- Rikicin zanga-zanga a Faransa ya tayar da muhawara kan baƙin haure a Kasar
- Shugaban Zambia ya bukaci a mayar da hankali kan hana rikice-rikice ta hanyar bunƙasa tattalin arziki
An kuma tsara haɗin gwiwa tsakanin Kamfanin Samar da Kayan Tsaro na Najeriya (DICON) da cibiyoyin tsaro na Rwanda.
A ganawarsa da Babban Hafsan Sojin Rwanda, Manjo Janar Vincent Nyakarundi, Shaibu ya ba da shawarar faɗaɗa musayar jami’an soji da horar da su kafin tura su ayyukan wanzar da zaman lafiya ta Cibiyar Martin Luther Agwai ta Jagoranci da Wanzar da Zaman Lafiya (MLAILPKC).

Shaibu ya bayyana ce sauran haɗin gwiwar sun haɗa da dabarun samar da kayan aiki, horar da ’yan sandan soja da musayar ƙwarewa kan yaƙi da ta’addanci da tawaye.
Ya ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen tunkarar sabbin matsalolin tsaro da inganta shirye-shiryen rundunonin sojin ƙasashen biyu.

A fannin samar da kayan tsaro, ya nemi a ƙarfafa haɗin gwiwar DICON da hukumomin Rwanda domin bunƙasa samar da kayan aikin soja a cikin gida da haɓaka fasaha.
Shaibu ya kuma yaba wa jarumtar sojojin Rwanda, musamman jami’an soja 600 da suka kare Kigali a lokacin kisan kiyashin da aka yi wa ’yan Tutsi a shekarar 1994.

A nasa ɓangaren, Nyakarundi ya yaba wa Sojin Najeriya bisa horar da jami’an Rwanda a fannonin ’yan sandan soja da tattara bayanan sirri.
Ya kuma nemi faɗaɗa horon ƙwarewar soja ta hanyar kwalejojin horar da hafsoshi da tsaro na Najeriya, tare da maraba da shirin musayar ɗalibai da haɗin gwiwar samar da kayan tsaro.