Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da ikon Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) na kama mutanen da take buƙatar bincikarsu, yayin da ta yi watsi da ƙarar tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin tauye haƙƙoƙinsa.
Mai shari’a Sylvanus Orji ya ce yunƙurin kama El-Rufai a Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe da ƙwace fasfo ɗinsa sun dace da ikon da doka ta bai wa hukumar DSS.
- Rikicin zanga-zanga a Faransa ya tayar da muhawara kan baƙin haure a Kasar
- Sojoji sun kuɓutar da mutane 11 daga hannun masu garkuwa da mutane a Kogi
Kotun ta kuma ce wasiƙun gayyatar da EFCC da ICPC suka aika wa tsohon gwamnan sun cika ƙa’idojin kundin tsarin mulki, kuma ba su keta haƙƙoƙinsa na asali ba.
El-Rufai ya nemi diyyar Naira miliyan 120 daga DSS, EFCC, ICPC da Babban Lauyan Tarayya, amma kotun ta yi watsi da ƙarar saboda rashin isassun hujjoji.
Alkalin ya kuma umarci a biya DSS, EFCC da ICPC Naira 200,000 kowannensu a matsayin kuɗin diyya.