Peter Obi ya ce Najeriya na buƙatar shugabanci da zai mayar da hankali kan samar da kayayyaki, bunƙasa tattalin arziki da rage talauci maimakon dogaro da amfani da abin da aka samar.
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar wani taron tattaunawa a ofishin Majalisar Turai kan Huldar Ƙasashen Waje (ECFR) da ke birnin Paris na Faransa.
- Kotu ta tabbatar da ikon hukumar DSS na kama El-Rufai
- Najeriya da Rwanda za su faɗaɗa horar da sojoji da samar da kayan tsaro
Taron ya haɗa masu tsara manufofi, jami’an diflomasiyya, ƙwararrun, wakilan ƙungiyoyin ƙasashen duniya da ’yan jarida domin tattauna makomar Najeriya da matsayinta a duniya.
Ya ce Najeriya tana da albarkatun ɗan Adam da na ƙasa da za su taimaka mata ta zama ƙasa mai tsaro da wadata, amma hakan na buƙatar shugabanci na gari da riƙon amana da fifita muradun jama’a.
Obi ya jaddada muhimmancin zuba jari a ilimi, lafiya da sana’o’in samar da kayayyaki, tare da ƙarfafa hukumomi da haɗin gwiwar ƙasashen duniya domin gina tattalin arzikin da zai amfani dukkan ’yan Najeriya.