Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi, sun kwato shanu 18 da aka sace, tare da kama waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi huɗu a Jihar Kebbi.
A ranar 18 ga Oktoba, 2026, dakarun sashe na biyu tare da ’yan sa-kai sun kai ɗauki ƙauyen Rambo da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu bayan samun rahoton harin ’yan ta’adda da suka shiga ƙauyen da niyyar yin garkuwa da mutane da satar shanu.
Bayan isa wurin, sojojin sun yi musayar wuta da maharan, inda suka samu nasarar ceto Suleiman Maiyaki Ikara, mai shekaru 40, tare da kwato shanu 18. Daga bisani, an miƙa mutumin da dabbobin ga shugaban gundumar Rambo.
- Najeriya da Rwanda za su faɗaɗa horar da sojoji da samar da kayan tsaro
- Kotu ta tabbatar da ikon hukumar DSS na kama El-Rufai
A wani samame da aka gudanar a wannan rana, sojojin tare da jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) sun kai farmaki wuraren da ake zargin ana safarar miyagun ƙwayoyi a Dakin Kowa, Karaye da Gubba, duk a Ƙaramar Hukumar Maiyama.
Samamen ya kai ga kama waɗanda ake zargi huɗu da kuma ƙwato wasu abubuwa da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.
A cewar sanarwar da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a ranar 19 ga Oktoba, an miƙa waɗanda aka kama da abubuwan da aka ƙwato ga ofishin NDLEA na Maiyama domin gudanar da bincike.