Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya musanta rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa yana shirin barin jam’iyyar ADC zuwa APC, yana mai bayyana ikirarin a matsayin marasa tushe.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Prince Daniel, ya sanya wa hannu a ranar 19 ga Oktoba, 2026, ofishin yaɗa labaran Tambuwal ya ce babu wani shiri na komawarsa APC.
- Kotu ta tabbatar da ikon hukumar DSS na kama El-Rufai
- Peter Obi ya ce Najeriya na buƙatar shugabanci da zai fifita inganta tattalin arziki
Sanarwar ta ce hotuna da bidiyoyin da ake yaɗawa ba su tabbatar da shirin sauya sheƙarsa ba, domin gaisawa ko hulɗa da ’yan wata jam’iyya ba yana nufin an kulla yarjejeniyar sauya sheƙa ba.
Ta ƙara da cewa Tambuwal na nan cikin ADC, inda ya mayar da hankali wajen ƙarfafa jam’iyyar, haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki da kuma shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Ofishin ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da masu sharhi a soshiyal midiya su tabbatar da irin waɗannan bayanai ta hanyar tuntuɓar ofishinsa kafin yaɗawa, yana mai cewa bai kamata a gabatar da rade-radi a matsayin sahihin labari ba.