Peter Obi ya tuno da waɗanda suka mutu a harin da aka yi wa masu zanga-zangar #EndSARS a ƙofar Lekki Toll Gate da ke Legas, yayin da ake cika shekaru shida da faruwar lamarin a ranar 20 ga Oktoba, 2026.
A cikin saƙon tunawa da ranar, Obi ya ce zanga-zangar ta kasance neman ingantacciyar ƙasa, inda ya jaddada cewa bai kamata a manta da waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda suka jikkata ba.
- ’Yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargin ’yan fashi ne a Ondo
- Peter Obi ya ce ba ya adawa da tallafin ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ga iyalansu
Ya ce har yanzu akwai buƙatar tabbatar da adalci, ɗaukar alhaki da mutunta haƙƙin bil’adama, yana mai cewa bai kamata a ɗauki zalunci a matsayin wani abu na yau da kullum ba.
Obi ya kuma yi kira da a gina Najeriya inda ake kare ’yan ƙasa maimakon cin zarafinsu, ana sauraron matasa maimakon tauye musu murya, kuma gwamnati ke amfani da ikonta cikin alhaki.
Ya bayyana fatansa na ganin an gina Najeriya inda ba za a sake hukunta kowane ɗan ƙasa saboda neman shugabanci nagari da kyakkyawar makoma ba.