Rundunar ’yan sandan Jihar Ondo ta kama mutum biyu da ake zargi da fashi da makami tare da ƙwato bindigogi ƙirar gida guda biyu a wasu samame daban-daban da ta kai a Akure, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Abayomi Jimoh, ya fitar a ranar 20 ga Oktoba, 2026, samamen farko an kai shi ne a ranar 13 ga Oktoba a hanyar Idanre, inda jami’an sintiri suka tsayar da wani mai shekaru 32, suka kuma gano bindiga ƙirar gida da aka ɓoye a tare da shi.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya amince da mallakar bindigar yayin tambayoyi, amma ana ci gaba da bincike domin gano inda ya samo ta da kuma dalilin mallakarta.
- Peter Obi ya ce ba ya adawa da tallafin ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ga iyalansu
- Tambuwal ya musanta shirin komawa APC
A wani samame da aka kai a ranar 19 ga Oktoba a yankin Madam Do Good, kan hanyar Oyemekun, Akure, ’yan sanda sun kama wani mai shekaru 35, bayan gano wata bindiga ƙirar gida a yayin binciken wasu mutane biyu da ke kan babur.
Rundunar ta ce ɗayan mutanen ya tsere, kuma ana ƙoƙarin cafke shi, yayin da ake ci gaba da bincike kan makaman da aka ƙwato da kuma yiwuwar alaƙarsu da aikata laifuka.
Komisishinan ’yan sandan jihar, Felix Ohagwu, ya yaba wa jami’an tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da sintiri da binciken sirri domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.