Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta gurfanar da mutum biyar da ake zargi da hannu a sace ɗalibai 20 da ke shirin shiga hidimar ƙasa ta NYSC da wani farar hula a Jihar Imo.

An gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Babbar Kotun Jiha ta Justice Oputa da ke Owerri, babban birnin jihar, bayan kama su a wasu samamen sirri da aka gudanar a jihohin Rivers da Abia.

An sace ɗaliban ne a ranar 1 ga Oktoba, 2026, kusa da Umunoha a Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, yayin da suke tafiya daga Ibadan ta Jihar Oyo zuwa sansanonin horas da masu hidimar ƙasa da aka tura su a jihohin Abia da Akwa Ibom.

A ranar 7 ga Oktoba, jami’an tsaro sun ceto ɗaliban 20 da farar hular a daji da ke Amakohia-Ubi, a Ƙaramar Hukumar Owerri West, inda daga bisani aka kai su asibitin DSS da ke Owerri domin duba lafiyarsu.

DSS ta ce ta kama mutum biyar ɗin ne tsakanin 10 zuwa 14 ga Oktoba a Fatakwal ta Jihar Rivers da Aba ta Jihar Abia, yayin da wasu mutum uku da ake zargi suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Ana ci gaba da farautarsu da sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a ƙungiyar masu garkuwa da mutane.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *