Majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar ADC ta ce kalaman Sanata Abdulaziz Yari, shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, sun nuna gazawar gwamnatin jam’iyyar wajen magance matsalar tsaro a Najeriya.
Yari ya yi tambayar cewa: “Idan Buhari, wanda tsohon soja ne, bai iya kawar da matsalar tsaro ba, me Tinubu zai iya yi?” A martaninta, ADC ta bayyana kalaman a matsayin abin da ke nuna rashin ƙarfin gwiwar APC wajen samar da mafita ga matsalar tsaro.
Jam’iyyar ta ce bayan kusan shekaru 12 da APC ta kwashe tana mulki, har yanzu ’yan Najeriya na fuskantar ta’addanci, garkuwa da mutane da kashe-kashe, yayin da al’ummomi ke rayuwa cikin fargaba.
- Tinubu ya ce ba zai dawo da tallafin man fetur ba
- DSS ta gurfanar da mutum biyar kan sace ɗaliban NYSC 20 a Imo
- Sojoji sun kuɓutar da mutane 27 da aka yi garkuwa da su a Katsina
ADC ta ce Najeriya na buƙatar shugabanci mai ɗaukar alhaki da samar da matakai na zahiri, ba uzuri kan matsalar tsaro ba.
Ta bayyana ɗan takararta, Atiku Abubakar, a matsayin wanda zai iya samar shugabanci na gari, tare da ƙarfafa tsarin tsaro, zamanantar da aikin ’yan sanda, amfani da fasaha da bayanan sirri, da samar da ayyukan yi ga matasa.
Jam’iyyar ta bukaci ’yan Najeriya su yi nazari kan kalaman Yari da tarihin APC wajen magance matsalar tsaro kafin zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Sanarwar, wadda daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Kola Ologbondiyan, ya sanya wa hannu, ta ce ƙasar na buƙatar sabuwar alkibla da za ta ba da fifiko ga tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.