Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi bayan ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a Abuja ranar 26 ga Oktoba, 2026, inda ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙara ta’azzara talauci da matsalolin tsaro a Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewa sama da ’yan Najeriya miliyan 140 na fama da talauci ta fannoni daban-daban, yana mai cewa cire tallafin man fetur da ƙarin basussukan gwamnati ba su haifar da ƙaruwa mai ma’ana a harkokin samar da kayayyaki ba.
- FRSC ta aika allunan lambobin rajistar motoci 19,560 zuwa Abuja cikin Oktoba
- Matawalle ya ce baje kolin AFRIDEX 2026 zai bunƙasa kera kayan tsaro a Najeriya
Obi ya ce idan aka zaɓe shi, zai jagoranci yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya aikata laifi bayan rantsar da sabuwar gwamnati ya fuskanci hukunci.
Ya kuma yi alƙawarin tarwatsa hanyoyin sadarwar masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga, tare da gano waɗanda ke ɗaukar nauyinsu.
Ɗan takarar ya kuma ce gwamnatinsa za ta mayar da mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon rikice-rikice zuwa garuruwansu cikin shekaru biyu na farko, tare da ƙarfafa tsaro da ’yancin zirga-zirga a faɗin ƙasar.