Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa da kudirin gyara dokar musayar fursunoni ta shekarar 2026, domin bai wa Najeriya damar aiwatar da yarjejeniyar musayar waɗanda aka yanke wa hukunci da ƙasashen da ba sa cikin Ƙungiyar Commonwealth.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar da Tinubu ya aika kan kudirin a zaman majalisar na ranar Talata, inda shugaban ƙasar ya buƙaci ’yan majalisar su gaggauta duba shi.
- Peter Obi ya yi alƙawarin mayar da Arewa cibiyar noma da masana’antu idan ya ci zaɓen 2027
- Tinubu ya nemi Majalisa ta amince da bashin waje na dala biliyan 20.5 da Yuro biliyan 1.05 domin ayyukan raya ƙasa
Kudirin na neman gyara dokar musayar waɗanda aka yanke wa hukunci wato Transfer of Convicted Offenders (Enactment and Enforcement) Act, Babi na T16 na dokokin Najeriya na shekarar 2004, domin sauƙaƙa aiwatar da yarjejeniyoyin da gwamnatin tarayya za ta kulla da sauran ƙasashe kan mayar da fursunoni.
Ɗaya daga cikin muhimman tanade-tanaden kudirin shi ne bai wa shugaban ƙasa ikon faɗaɗa amfani da dokar zuwa ƙasashen da Najeriya ta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da su, ta hanyar fitar da umarni a Federal Gazette.
A cewar Tinubu, gyaran zai samar da tushen doka wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da Najeriya za ta kulla da ƙasashen da ba sa cikin Commonwealth.
Sai dai kudirin na buƙatar amincewar Majalisar Dokoki ta Ƙasa kafin ya zama doka.