Wani rahoton bincike ya bayyana cewa jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) a Jihar Neja sun kasa ɗaukar matakin gaggawa duk da kukan neman taimako da fursunoni suka riƙa yi kafin mutuwar mutane 33 a ofishin hukumar da ke Minna a watan Satumbar 2026.
Rahoton ya ce an tsare kusan maza 50 a cikin ɗaki mai faɗin murabba’in mita 12, wanda ba shi da isasshen iska, ruwan sha ko bandaki mai aiki.
An kuma tsare manya da ƙananan yara a wuri ɗaya, yayin da yanayin zafi da cunkoso suka ƙara tsananta.
- Tinubu ya nemi Majalisa ta faɗaɗa yarjejeniyar musayar fursunoni zuwa ƙasashen wajen Commonwealth
- Tinubu ya nemi Majalisa ta amince da bashin waje na dala biliyan 20.5 da Yuro biliyan 1.05 domin ayyukan raya ƙasa
A cewar kwamitin karkashin shugabancin tsohun daraktan hukumar NSCD Jonathan Kure, ya ce binciken ya gano cewa, alamun damuwa sun fara bayyana bayan ƙarfe 7 na yamma a ranar 16 ga Satumbar 2026, inda fursunonin suka riƙa bugun ƙofofi da bango, suna ihu tare da roƙon a ba su ruwa.
Rahotun ya ce jami’an da ke kusa sun ji kukan, amma ba a buɗe ɗakin ko rage cunkoson ba.
Kwamitin ya ce mutuwar ta faru ne tsakanin ƙarfe 8 na dare ranar 16 ga Satumba da ƙarfe 7 na safe ranar 17 ga Satumba.
Binciken ya tabbatar da mutuwar mutane 33, ciki har da yara 14, yayin da mutane 41 suka tsira.
Rahoton ya danganta mutuwar da ƙarancin iska, cunkoso, zafi da rashin ruwa, ba wai barkewar cuta ba.
Kwamitin ya bayyana cewa lamarin ya kasance abin da za a iya kauce wa faruwarsa, tare da ba da shawarar ɗaukar matakan ladabtarwa kan jami’an da ke da alhaki, inganta wuraren tsare mutane da kuma ƙarfafa sa ido kan yadda ake kula da waɗanda ke hannun hukumar.