Wani kwamitin bincike mai zaman kansa ya ba da shawarar korar jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) da aka gano suna da babban alhaki kan mutuwar fursunoni 33 a ofishin hukumar da ke Minna, Jihar Neja, a watan Satumbar 2026.

Rahoton ya kuma bukaci a gurfanar da jami’an da bincike ya tabbatar sun aikata laifuka, ciki har da kisan kai, sakaci na laifi, azabtarwa da mu’amala ta rashin mutuntaka, gwargwadon laifin da aka tabbatar da kuma tanadin doka.

Kwamitin karkashin shugabancin tsohun daraktan hukumar NSCD Jonathan Kure, ya bayyana cewa kwamandan NSCDC na Jihar Neja, CC Suberu Aniviye Siyaka, ya amince da gudanar da aikin ba tare da cikakken shiri da kulawar da ta dace ba.

Rahoton ya kuma zarge shi da kasa tabbatar da bin ƙa’idojin tsare mutane da kuma fitar da sanarwar da ta danganta mutuwar da barkewar cuta, duk da cewa binciken bai gano hujjar da ke tabbatar da hakan ba.

Haka kuma, rahoton ya bayyana gazawar wasu jami’ai wajen kula da fursunonin da kuma ɗaukar matakin gaggawa lokacin da suka fara kukan neman agaji.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar gudanar da bincike kan zarge-zargen karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da kuma rashin kyakkyawan tsarin kula da kayayyakin shaida.

Baya ga hukunta waɗanda ke da alhaki, kwamitin ya bukaci a sake fasalin shugabancin NSCDC tare da inganta horo, sa ido da tsarin kula da fursunoni.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *