Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya bayyana cewa ya samu ziyarar bazata daga Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-ƙirƙire ta Najeriya, Hannatu Musawa, a ofishinsa da ke Abuja.
Rabiu ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce Musawa, wadda ya kira tsohuwar matarsa, ta kai masa ziyara a ranar Laraba.
- ’Yan sanda sun miƙa buhunan ganyen da ake zargin tabar wiwi ne 69 ga NDLEA
- Jihar Jigawa ta tura ɗalibai 65 China karatun digiri na biyu kan noma
Ya ce duk da sauyin da lokaci ke kawowa, abota da mutunta juna suna nan daram, yana mai bayyana farin cikinsa da sake ganinta.
Rabiu ya yaba wa Musawa bisa himma da jajircewar da take nunawa wajen bunƙasa al’adu da tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire a Najeriya.
Ya kuma yi mata fatan ci gaba da samun nasara a ayyukanta.