Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi a ɓangaren ilimi na ƙara buɗe damar karatun gaba da sakandare, koyar da sana’o’i da inganta horas da malamai a Najeriya.
Idris ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis, 29 ga Oktoba, 2026, yayin taron kwamitin shugabannin kwalejojin horas da malamai na gwamnatin tarayya.
Darakta-Janar na NTA, Salihu Abdulhamid Dembos, ne ya gabatar da jawabin ministan a madadinsa.
- Sojojin Nigeria sun dakile harin kwanton ɓauna a Zamfara, sun kwato dabbobi 520 a Sokoto
- Manyan ayyukan more rayuwa za su taimaka wa Najeriya cimma tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya – Tinubu
Ministan ya ce Asusun Ba da Lamunin Karatu na Ƙasa (NELFUND) na taimaka wa ɗaliban da suka cancanta wajen biyan kuɗin karatun gaba da sakandare, yayin da shirin koyar da sana’o’i (TVET) ke bai wa matasa ƙwarewar da za su yi amfani da ita wajen samun aikin yi ko kafa sana’o’insu.
Ya jaddada cewa nasarar sauye-sauyen ilimin ta dogara da samun ƙwararrun malamai da ingantaccen shugabanci a makarantu.
Ya kuma buƙaci shugabannin kwalejojin da su tabbatar da gaskiya, riƙon amana, kula da dukiyar makarantu da kyakkyawar alaƙa da masu gudanar da harkokinsu.
Idris ya ce ya kamata kwalejojin su ƙarfafa koyar da ɗabi’un ƙasa, kishin al’umma da tunani mai zurfi, domin taimaka wa matasa bambance gaskiya da ƙarya, mutunta bambance-bambance da kuma bayar da gudummawa wajen zaman lafiya da haɗin kan Najeriya.