Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kammala horar da jami’anta kan kula da tsaron zaɓe na tsawon kwanaki biyar, a wani ɓangare na shirin horas da jami’ai 10,000 a faɗin ƙasar.

Rundunar ta gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar Asusun Tallafa wa ’Yan Sanda na Najeriya (NPTF), inda matakin farko ya shafi jihohi 18 da Babban Birnin Tarayya Abuja.

A lokacin buɗe shirin, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya umarci jami’an da za a tura aikin zaɓe da su kasance tsaka-tsaki, ƙwarewa da riƙon amana, tare da kare masu zaɓe da jami’an zaɓe ba tare da nuna bambanci ba.

Horon ya ƙunshi dokokin zaɓe, hanyoyin sadarwa, tattara bayanan sirri, tantance barazana da kuma nauyin da doka ta ɗora wa ’yan sanda.

An kuma jaddada muhimmancin bin doka, rashin nuna bambanci da haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro gabanin zaɓukan 2027.

A sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, CSP Ani Iniedu, ya fitar ranar 2 ga Nuwamba, rundunar ta ce mahalarta sun yi alƙawarin amfani da ilimin da suka samu wajen kare haƙƙin masu zaɓe da kuma mutuncin tsarin zaɓe, tare da yaɗa abubuwan da suka koya ga sauran jami’ai.

Rundunar ta kuma jaddada aniyarta ta ci gaba da horas da jami’ai domin tabbatar da tsaro yayin da ’yan Najeriya ke gudanar da haƙƙinsu na zaɓe.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *