Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar wayoyin lantarki masu sulke a yankin Guzape, tare da kwato wasu daga cikin wayoyin da aka yanke.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare ranar 31 ga Oktoba, 2026, yayin da jami’an ’yan sanda ke sintiri a titin Walter Ofonagoro da ke Guzape. A lokacin ne suka ga motocin Lexus SUV da Toyota Sienna ajiye a wani wuri cikin yanayin da ya tayar musu da hankali.

Sanarwar rundunar ta ce mutanen da ke cikin motocin sun yi gudun su tsere bayan ganin jami’an, inda suka bar wani abokinsu da ya yi ƙoƙarin tserewa da ƙafa, sai dai jami’an sun bi shi tare da kama shi, sannan suka binciki wurin da suka gan su, inda suka gano wayoyin lantarki masu sulke da aka yanke.

Binciken farko ya nuna cewa wanda aka fara kamawa na cikin wata ƙungiyar da ake zargi da lalata kayayyakin more rayuwa na gwamnati da na masu zaman kansu a wuraren da ba su da cunkoso a Abuja.

Daga baya, binciken ya kai ga kama wani mutum da ake zargi da hannu a lamarin, wanda ya tsere da ɗaya daga cikin motocin.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran ’yan ƙungiyar da kuma kama waɗanda suka tsere.

Ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da buƙatar mazauna Abuja su riƙa kai rahoton duk wani motsi ko mutum da suka zargi da aikata laifi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *