An fitar da sunayen ’yan wasa 26 da aka tantance domin zaɓen tawagar ’yan wasan duniya 11 ta FIFPRO, inda fitattun ’yan wasan duniya Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ke cikin jerin.

’Yan wasan ƙwallon ƙafa 19,806 daga ƙasashe 73 ne suka kaɗa ƙuri’a wajen zaɓen waɗanda suka taka rawar gani, kamar yadda aka bayyana a sanarwar fitar da jerin sunayen.

Sauran ’yan wasan da aka tantance sun haɗa da Thibaut Courtois, Emiliano Martínez, David Raya, Pau Cubarsí, Marc Cucurella, Virgil van Dijk, Gabriel Magalhães, Achraf Hakimi, Nuno Mendes, William Saliba da Dayot Upamecano.

A ɓangaren tsakiyar fili kuwa, an samu Jude Bellingham, Bruno Fernandes, Enzo Fernández, Pedri, Declan Rice, Rodri da Vitinha, yayin da Erling Haaland, Harry Kane, Khvicha Kvaratskhelia, Kylian Mbappé, Lamine Yamal da Michael Olise ke cikin waɗanda aka tantance a ɓangaren masu kai hari.

FIFPRO Men’s World 11 wata tawaga ce da ake zaɓa bisa ƙuri’un ’yan wasan ƙwallon ƙafa na ƙwararru, domin karrama waɗanda suka nuna bajinta a fagen tamaula.

Jerin sunayen 26 ɗin shi ne matakin tantancewa kafin fitar da ’yan wasan da za su shiga tawagar ƙarshe.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *