Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce ta kuɓutar da mata masu shayarwa uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Kogi, bayan wani harin da aka kai wa motar haya a kusa da garin Ebiya da ke ƙaramar hukumar Ajaokuta.
A cikin sanarwar rundunar, ta ce ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:17 na dare a ranar 1 ga Nuwamba, 2026, dangane da harin da wasu ’yan bindiga suka kai wa motar Toyota Hummer Bus.
- ’Yan sanda sun gano gawar jami’ai biyar da ’yan bindiga suka kashe a Zamfara
- Ɗan Cristiano Ronaldo ya samu kiran farko zuwa tawagar Portugal ta ’yan ƙasa da shekara 17
Rundunar ta ce jami’anta sun jagoranci jami’an tsaro na haɗin gwiwa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka tarar da gawar wani fasinja da ya mutu sakamakon harbin bindiga.
Ta bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da fasinjoji 13 zuwa cikin daji, amma jami’an tsaro sun samu nasarar kuɓutar da mata masu shayarwa uku tare da gano motar da aka kai wa harin.
Rundunar ta ce ana ci gaba da aikin bincike da tsefe daji domin kuɓutar da sauran waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya, tare da cafke waɗanda suka kai harin.