Jam’iyyar APC reshen Jihar Osun ta nuna rashin gamsuwa da yadda aka tsara mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ta nemi a sake duba jerin sunayen domin shigar da ƙarin ’ya’yan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran jam’iyyar na jihar, Wole Adunola, da wasu mambobin kwamitin gudanarwa suka fitar, sun nuna damuwa kan cire wasu mambobin kwamitin gudanarwa na jihar, waɗanda a cewarsu ya kamata su kasance cikin mambobin kwamitin kamfen bisa matsayinsu.

Sanarwar ta kuma ce tsarin ya yi hannun riga da umarnin da aka ce shugaban ƙasa ya bayar a baya, wanda ya bayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar.

Reshen jam’iyyar ya kuma nuna rashin fahimtarsa kan ƙaddamar da wani babban kwamitin kamfen da zai jagoranci yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a faɗin jihar, yana mai cewa ba a yi cikakken bayani kan dalilin samar da sabon tsarin ba.

APC ta Osun ta ce akwai buƙatar fayyace ayyuka da nauyin da ke kan kowanne kwamiti, tare da tabbatar da cewa an daidaita tsarin domin guje wa ruɗani da kuma haɗa kan ’ya’yan jam’iyyar wajen yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *