Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin sake buɗe iyakokin Najeriya da ƙarfafa dangantakar ƙasar da maƙwabtanta na Afirka idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin bikin fara yaƙin neman zaɓensa a hukumance a jihar Sakkwato, inda ya ce zai sake duba batun rufe iyakokin ƙasar.

Ya ce sake buɗe iyakokin zai taimaka wajen dawo da kyakkyawar dangantakar Najeriya da ƙasashen da ke makwabtaka da ita.

Ɗan takarar ya kuma bayyana aniyarsa ta farfaɗo da haɗin gwiwar da ke tsakanin Najeriya da sauran ƙasashen Afirka, musamman wajen harkokin kasuwanci da hulɗar ƙasashen biyu.

Rahoton Bashir Ibrahim Nababa ya ce Atiku ya bayyana wannan alƙawari ne a wajen taron ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a Sakkwato.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *