Majalisar Masarautar Gaya da ke Jihar Kano ta dakatar da Dagacin ƙauyen Shagogo, Abbas Ibrahim, bisa zargin aikata manyan laifukan rashin da’a.
An bayyana dakatarwar ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran masarautar, Jamilu Adamu, ya fitar a ranar Laraba.
- Gwamnan Edo da Sarkin Benin sun goyi bayan yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi
- Atiku ya yi alƙawarin buɗe iyakokin Najeriya idan ya ci zaɓen 2027
Sanarwar ta ce Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim, ne ya sanar da matakin dakatar da dagacin.
Sai dai, ba a bayyana tsawon lokacin da dakatarwar za ta ɗauka ba.