Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta jam’iyyar APC ta ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi a ɓangaren ilimi sun taimaka wajen faɗaɗa damar samun ilimi, inganta walwalar malamai da daidaita jadawalin karatu a manyan makarantun Najeriya.
A cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Dele Alake, ya fitar a ranar 4 ga Nuwamba, 2026, jam’iyyar ta ce rahoton Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya na shirin sabunta harkokin ilimi (NESRI) na 2026 ya nuna cewa gwamnatin ta ware Naira tiriliyan 3.52 ga ilimi a kasafin kuɗin 2026, tare da samar da tallafin dala miliyan 552 domin inganta ilimin firamare da sakandare.
Ta kuma ce shirin BESDA ya taimaka wajen mayar da sama da yara miliyan ɗaya da ba sa zuwa makaranta cikin ajujuwa.
- Musulmai takwas za su wakilci al’ummarsu a Majalisar Dokokin Amurka – Ilhan Omar
- Sarkin Musulmi ya karɓi baƙuncin Atiku Abubakar a fadarsa da ke Sakkwato
Sanarwar ta ce shirin bayar da horo kan sana’o’i da fasaha na TVET ya samu sama da mutane miliyan 2.8 da suka nemi shiga, inda aka tantance mutum 156,446 da ke samun horo kyauta, alawus na wata-wata da tallafin fara sana’a.
Haka kuma, ta ce an riga an fitar da Naira biliyan 65.7 ga waɗanda ke samun horon, yayin da aka bai wa cibiyoyin horaswar Naira biliyan 30.2.
Game da tallafin karatu, APC ta ce Asusun Bayar da Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) ya sarrafa buƙatun lamuni 1,659,853 tare da bayar da Naira biliyan 372.62 ga ɗalibai a manyan makarantu 319.
Sanarwar ta ce cikin kuɗin, Naira biliyan 192.89 na kuɗin makaranta ne, yayin da Naira biliyan 179.73 suka kasance alawus na kula da kai.
Jam’iyyar ta kuma ce gwamnati na kashe Naira biliyan 110 wajen gyaran makarantun koyon aikin likitanci na tarayya 18, yayin da adadin ɗaliban da ke karatun aikin jinya ya ƙaru daga 81,480 a 2023 zuwa 114,300 a 2025.
Ta ƙara da cewa an bayar da Naira biliyan 2.5 ga ɗalibai 45 masu sana’o’in kirkire-kirkire ta hanyar shirin tallafa wa harkokin kasuwancinsu.
Da yake tsokaci kan nasarorin, Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya ce ba yawan kuɗin da aka ware ko shirye-shiryen da aka ƙaddamar ne kaɗai za su nuna nasarar gyare-gyaren ba, sai dai tasirinsu ga ɗalibai, malamai da cibiyoyin ilimi.