Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutane 20 a ƙauyen Akwando da ke yankin Kuturmi, ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 12 na dare ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamban 2026, lokacin da mazauna ƙauyen ke cikin gidajensu.

Ƙungiyar raya yankin Kuturmi (KUDA) ta bayyana sunayen waɗanda aka kashe da suka haɗa da Irimiya Galadima, mai shekara 41, da Benjamin Danlami, mai shekara 32.

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Dakta Joseph Ariko, da sakataren yaɗa labaranta, Manasseh Samuel Akwando, suka sanya wa hannu, ta kuma fitar da sunayen mutane 20 da ta ce an sace.

KUDA ta bayyana damuwarta kan yawaitar hare-hare a yankin, tana mai cewa al’ummomin Ariko da Awon ma sun fuskanci irin waɗannan hare-hare a baya, inda aka kashe mutane tare da yin garkuwa da wasu.

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa ‘yan bindiga na hana mazauna yankin shiga gonakinsu ba tare da sun biya kuɗi ba.

Ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna da su ƙarfafa tsaro a yankin, su kuma gudanar da samame domin kuɓutar da waɗanda aka sace.

A wani labarin makamancin haka, wasu mazauna Babban Saura PW da ke Millennium City, a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, da aka sace tun ranar 1 ga watan Oktoban 2026, na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa.

Daga cikinsu akwai Hafsat Sikiru da ɗanta Abdulsalam, waɗanda mijinta, Sikiru Shuaibu, ya mutu yayin ƙoƙarin kare iyalinsa daga maharan.

Wannan na zuwa ne duk da ceto wasu mutane takwas da jami’an tsaro suka yi a wani samame a cikin daji, ciki har da wata mata mai juna biyu da aka sace a Millennium City.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *