Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama mutum takwas bisa zargin hannu a lalata da satar kayayyakin more rayuwa, ciki har da sandunan fitilun tituna.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce jami’an ’yan sanda sun kama mutanen ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare a ranar 23 ga Oktoba, 2026, yayin sintirin yaƙi da laifuka a cikin birnin.

Ta bayyana cewa binciken farko ya nuna waɗanda ake zargin mambobin wata ƙungiyar masu aikata laifuka ne da ta ƙware wajen lalata da satar kayayyakin gwamnati da na masu zaman kansu a yankunan Central Business District, Maitama, Wuse, Garki da Asokoro.

Rundunar ta ce ta kwato dogayen sandunan fitilun titi guda biyar da aka yanke daga gindinsu, waɗanda ake zargin an sace ne.

A halin yanzu, waɗanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato suna hannun ’yan sanda.

Rundunar ta ƙara da cewa za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, tare da kira ga mazauna Abuja da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suka gani na shakku ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *