UNICEF ta ce tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, hare-haren da aka tabbatar sun lalata ko katse ayyukan samar da ruwa da tsaftar muhalli sun ninka har sau uku.
Rahotonta mai suna Water Under Fire: Volume 4 ya yi nazari kan hare-haren da aka samu a ƙasashe da yankuna 23 tsakanin Janairun 2021 da Yunin 2026.
Ta bayyana cewa lalata ko katse hanyoyin samar da ruwa na haddasa yaɗuwar cututtuka kamar kwalara, ciwon hanta da gudawa mai tsanani, tare da ƙara matsalar rashin abinci mai gina jiki.
- Tinubu da Shettima sun isa Uyo domin halartar gangamin APC
- ’Yan sanda sun kama mutum takwas bisa zargin satar sandunan fitilun tituna a Abuja
Haka kuma, asibitoci da cibiyoyin lafiya na kasa gudanar da ayyukansu, yayin da wasu makarantu ke rufewa saboda ƙarancin ruwa.
Asusun ya kuma bayyana cewa yara, musamman ’yan mata, na fuskantar barazanar sacewa, cin zarafi da tilasta musu shiga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai yayin da suke tafiya nesa da gidajensu domin samo ruwa.
Hakan na kuma hana su zuwa makaranta tare da ƙara fuskantar barazanar aikin dole da aurar da su da wuri.
A rahoton, UNICEF ta ce tana taimaka wa al’ummomi da hukumomin yankin wajen gyara hanyoyin samar da ruwa, amfani da makamashin hasken rana da gina kayayyakin more rayuwa da za su iya jure tasirin rikice-rikice.
Ta kuma yi kira da a samar da tsarin tattara bayanan hare-haren da ake kai wa hanyoyin ruwa, kare ma’aikatan samar da ruwa da kuma tabbatar da isar da agajin jinƙai ga al’ummomin da abin ya shafa.