Daruruwan magoya bayan jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na Jihar Yobe sun taru a Damaturu, babban birnin jihar, domin gudanar da gangamin nuna goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.
Gangamin, wanda Farfesa Sheriff Almuhajir, mai kula da ƙungiyar Tinubu Must Go Again ta ƙasa, ya shirya, ya samu halartar ’yan jam’iyya, masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da mambobin ƙungiyar daga ƙananan hukumomi 17 na jihar.
- ADC ta bukaci ’yan Najeriya su yi koyi da Amurkawa kan tsadar rayuwa a zaɓen 2027
- Gwamnatin tarayya ta hana NTI Kaduna karɓar sababbin ɗalibai a 2026
Farfesa Almuhajir ya ce an shirya gangamin ne domin wayar da kan jama’a da ƙara samun goyon baya da ƙuri’u ga Tinubu, yayin da yake neman wa’adi na biyu, da kuma sauran ’yan takarar APC a zaɓen mai zuwa.
Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Jihar Yobe za ta ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai wajen nuna goyon baya ga sake zaɓen shugaban ƙasar da nasarar sauran ’yan takarar APC a 2027.
Daga cikin manyan baki da suka halarci gangamin akwai Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe, Dakta Muhammad Goje, da Kwamishinan ƙungiyar na jihar, Dakta Muktar Yerima, da sauran masu ruwa da tsaki.