Kasar Sin ta kakaba sabbin dokoki da za su bai wa hukumomi damar cin tarar har Yuan 100,000, kwatankwacin dalar Amurka 14,000, ga masu amfani da takardun ƙarya wajen ikirarin ƙwarewa da bayar da shawarwari a kafafen sada zumunta.
Dokokin da Hukumar Kula da Harkokin Intanet ta ƙasar (CAC) ta bullo da su sun shafi masu wallafa bayanai kan fannoni kamar lafiya, harkokin kuɗi, shari’a da ilimi, inda aka buƙaci su tabbatar da cancantarsu kafin su riƙa bayar da shawarwari.
A ƙarƙashin dokokin, masu wallafa bayanai za su gabatar da shaidar karatunsu, lasisin ƙwarewa ko takardar horon da suka samu a fannin da suke magana a kai.
- Sowore ya zargi Tinubu da shirin hana gudanar da sahihin zaɓe a Najeriya
- Trump ya ce Amurka a shirye take ta sake ɗaukar manyan matakai a binciken sararin samaniya
Haka kuma, kafafen sada zumunta irin su Douyin, Weibo da Bilibili za su riƙa tantance cancantar masu wallafa irin waɗannan bayanai, yayin da waɗanda suka yi amfani da takardun ƙarya za su iya rasa asusunsu ko fuskantar dakatarwa ta dindindin.
Mahukuntan China sun ce matakin na da nufin dakile yaɗuwar bayanan da ba su da inganci da kuma kare masu amfani da kafafen sada zumunta daga shawarwarin da ka iya cutar da lafiyarsu, dukiyoyinsu ko makomarsu.
A cewar Aderemi Ogunpitan, tasiri da yawan mabiya a kafafen sada zumunta ba su maye gurbin ilimi da ƙwarewar da ake buƙata wajen bayar da shawarwari kan muhimman fannoni ba.