Kamfanin siminti na Dangote da ke Obajana, Jihar Kogi, ya tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa 15 tare da girka na’urar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai ƙarfin 3.6kW domin inganta rayuwar mazauna yankin.

Sanarwar da kamfanin ya fitar, ta ce an gudanar da waɗannan ayyuka ne a yayin makon wayar da kan jama’a kan muhalli da ci gaba mai ɗorewa na shekarar 2026, wanda ya mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arzikin al’umma da inganta samar da makamashi mai tsafta.

A ɓangaren tallafa wa ’yan kasuwa, kamfanin ya shirya horaswa kan dabarun bunƙasa sana’o’i, sarrafa kuɗi, kyautata hulɗa da kwastomomi da kuma gudanar da kasuwanci cikin ɗorewa, tare da karrama ƙananan kamfanoni 15 da lambobin yabo.

Haka kuma, kamfanin ya ƙaddamar da na’urar hasken rana mai ƙarfin 3.6kW a yankin Oyo, domin taimakawa wajen samar da wutar lantarki ga kayayyakin aikin samar da ruwa a yankin.

Sanarwar ta bayyana cewa ana sa ran na’urar za ta inganta ingancin samar da ruwan sha, rage dogaro da hanyoyin samar da makamashi na gargajiya tare da ƙara samun damar amfani da wannan muhimmin abin more rayuwa.

Kamfanin ya ce shirye-shiryen na daga cikin ƙoƙarinsa na tallafa wa al’ummomin da ke maƙwabtaka da masana’antarsa, ta hanyar ƙarfafa sana’o’i, samar da makamashi mai tsafta da inganta rayuwar jama’a.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *