Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’addar Boko Haram/ISWAP biyu tare da ƙwato bindigogi da wasu makamai, bayan dakile wani harin ta’addanci a Jihar Adamawa.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 8 ga Nuwamba, 2026, a mahadar Zangula Kilba da ke ƙaramar hukumar Gombi, inda sojojin suka fatattaki maharan tare da tilasta wa sauran tserewa.

Bayan fafatawar, sojojin sun ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu, harsasai 115, da wasu kayan haɗa bama-bamai.

Sun kuma ƙwato wasu kayayyaki da suka haɗa da wayar Android da kuɗi Naira 15,000.

A wani samame kuma, a ranar 9 ga Nuwamba, sojojin da ke Mubi sun kuɓutar da wata mata mai suna Happiness Dama Dauda, wadda wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace a gonarta da ke Dutse-Uku, ƙaramar hukumar Mubi ta Kudu.

Rundunar ta ce haɗin gwiwar sojoji da mafarauta da kuma bin sawun masu garkuwar ya kai ga kuɓutar da wasu mutane biyu da ake zargin an sace su tun da farko, wanda ya kai adadin waɗanda aka ceto zuwa uku.

An kuma gano babur, adaidaita sahu ɗauke da buhunan wake 15 da motar ɗaukar kaya ɗauke da buhunan gyada 13, tare da mayar da su ga masu su.

Rundunar ta ce dakarunta na ci gaba da sintiri da sa ido a yankin domin hana ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka samun damar kai hare-hare.

Ta kuma jaddada muhimmancin musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma wajen yaƙi da ta’addanci.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *