Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) tare da Hukumar kula da ’yan gudun hijira da ƙaura (NCFRMI) sun karɓi ’yan Najeriya 175 da suka dawo daga birnin Misrata na ƙasar Libya.
Mutanen sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja, Jihar Legas, da misalin ƙarfe 4:32 na yammacin Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026, ta jirgin saman Air Buraq Airlines.
Cikin waɗanda suka dawo akwai manya 167, maza 109 da mata 58, yara huɗu, jariri namiji guda da kuma mutane uku masu matsalolin lafiya, waɗanda suka haɗa da namiji ɗaya da mata biyu.
- Tinubu ya taya jakadan Najeriya a Rasha murnar cika shekara 70 da haihuwa
- Al’ummar Rimin Kebbe da matasan Kano sun yaba wa ’yan sanda kan yaƙi da ’yan daba
Hukumar NEMA ta ce an gudanar da rajistar bayanan halittar jikin waɗanda suka dawo da kuma tantance su ta hannun jami’an hukumar shige da fice ta Najeriya domin tabbatar da bayanansu da taimaka musu wajen sake farawa da rayuwa.
An kuma ba su tallafin jin kai da suka haɗa da abinci, ruwan sha, duba lafiyarsu da motocin ɗaukar marasa lafiya ga waɗanda ke buƙatar kulawa ta musamman.
Shirin dawo da mutanen ya gudana ne ƙarƙashin tsarin komawa gida bisa son rai (AVR), wanda ƙungiyar ƙasa da ƙasa mai kula da ƙaura (IOM) ke gudanarwa tare da gwamnatin tarayyar Najeriya, domin taimaka wa waɗanda suka dawo su koma cikin al’ummominsu.