Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce alƙawarin ba kansilolin da suka yi nasarar jawo goyon bayan al’ummominsu ga Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 kyautar Naira miliyan 10 kowannensu, ba yunƙurin sayen ƙuri’u ba ne.
Wike ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin rangadin duba ayyukan raya ababen more rayuwa a Abuja, inda ya ce akwai bambanci tsakanin ba da lada ga masu gudanar da gangamin siyasa da kuma ba wa masu zaɓe kuɗi domin su zaɓen ɗan takara.
Ministan ya ce bai umarci kansilolin su karɓi kuɗi su raba wa masu zaɓe ba, sai dai ya ƙalubalanci su da su nuna ƙwazo wajen neman goyon bayan jama’a. Ya ce za a ba su ladan ne idan sun samu nasarar cimma wannan buri.
- Al’ummar Rimin Kebbe da matasan Kano sun yaba wa ’yan sanda kan yaƙi da ’yan daba
- Sojoji sun kashe ’yan ta’adda biyu, sun kuɓutar da mutane uku a Adamawa
Ya kwatanta alƙawarin da kyaututtukan da ake yi wa ’yan wasa idan suka lashe gasannin ƙasa da ƙasa, yana mai cewa irin wannan tukuici na ƙarfafa himma da jajircewa.
Wike ya kuma soki wasu kafafen yaɗa labarai bisa abin da ya kira rashin bambance lada ga masu aikin siyasa da kuma sayen ƙuri’u.
Ya ce ana kashe kuɗi wajen tallata ’yan takara da jam’iyyun siyasa, amma ba a fassara hakan a matsayin sayen ƙuri’u kai tsaye.
A yayin rangadin, ministan ya bayyana gamsuwarsa da yadda ayyukan ISEX 2, Southern Parkway da titin S1, wanda ya ƙunshi tashar kashe gobara, ke gudana.
Ya ce ana sa ran kammala ayyukan kafin 15 ga Disamba, yana mai cewa ayyukan raya ƙasa na gwamnatin Tinubu na daga cikin abubuwan da za su gabatar yayin neman wa’adin mulki na biyu.