Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 28 ga Nuwamba, 2026, domin gudanar da gwajin tantance masu zaɓe a dukkan jihohin Najeriya, a wani mataki na tabbatar da ingancin na’urorin BVAS da tsarin tura sakamakon zaɓen 2027.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a cibiyar Chatham House da ke Landan ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Kimpact Development Initiative (KDI).
Ya ce gwajin zai taimaka wajen tabbatar da cewa tsarin tantance masu zaɓe da tura sakamakon zaɓe ta hanyar na’ura na aiki yadda ya kamata kafin gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa.
- Majalisar Wakilai ta ware Naira miliyan 100 ga ’yan wasan Flamingos bayan lashe Kofin Duniya
- APC ta yi Allah-wadai da hare-haren tarukan siyasa, ta buƙaci kama waɗanda suka aikata su
- ECOWAS ta nemi ƙarfafa haɗin gwiwar soji da Najeriya don magance matsalolin tsaro a yammacin Afirka
Amupitan ya bayyana cewa hukumar ta rage adadin masu zaɓen da za a tantance da kowace na’urar BVAS daga 1,250 zuwa 850, tare da sayen ƙarin na’urori domin sauƙaƙa ayyukan tantance masu zaɓe. Ya ce rumfunan da ke da masu zaɓe sama da 850 za su samu na’urori fiye da ɗaya.
Ya kuma ce INEC ta samar da sabbin matakan kariya a tsarin tattara sakamako, domin hana aika sakamakon da bai dace ba ko kuma wanda ke ɗauke da ƙuri’un da suka wuce adadin masu zaɓe zuwa shafin IReV.
Haka kuma, hukumar na gina wuraren ajiyar na’urori masu kula da yanayin zafi a dukkan jihohi, bayan matsalolin da zafi ya haifar wa BVAS a zaɓen 2023.
Shugaban INEC ya ƙara da cewa hukumar ta samu wani kaso mai yawa na kuɗin gudanar da zaɓen 2027, amma tana jiran sakin ragowar kuɗaɗen, waɗanda wani ɓangare daga cikinsu zai tafi wajen ɗaukar ma’aikatan wucin gadi da kula da jin daɗinsu.
Ya ce an tabbatar wa hukumar cewa za a fitar da kuɗin kafin ƙarshen Nuwamba.