Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da harin da wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne suka kai wa mambobi da magoya bayan jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a yankin Oregun da ke Ikeja, Jihar Legas.

Harin, wanda ya jikkata mutane fiye da goma sha biyu, ya kuma tarwatsa shirye-shiryen gudanar da taron tattaunawa da jama’a da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar, Peter Obi, da mataimakinsa, Rabi’u Musa Kwankwaso, za su halarta.

A cikin sanarwarta, Amnesty International ta buƙaci hukumomi su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa duk waɗanda ake zargi da hannu a harin sun fuskanci shari’a ta gaskiya, ba tare da amfani da hukuncin kisa ba.

Ta ce yawaitar hare-hare kan jam’iyyun adawa da harkokinsu na siyasa na tauye ’yancin jama’a na haɗuwa da ƙungiyoyi.

Ƙungiyar ta ce harin ya faru ne a cibiyar taro ta Classique da ke kan titin Kudirat Abiola Way, Ikeja, inda aka lalata wurin tare da barin jini a ƙasa.

Ta kuma bayyana cewa maharan sun yi amfani da adduna da wuƙaƙe, lamarin da ya tilasta wa shaguna rufewa tare da haddasa cunkoson ababen hawa a yankin.

Amnesty International ta ce ta samu rahotanni tare da tantance wasu hujjojin bidiyo da ke nuna yadda aka kai irin waɗannan hare-hare a wasu sassan ƙasar.

Ta kuma ce bidiyoyin da ta samu sun nuna wasu mutane na kewaye da magoya bayan NDC tare da dukansu da sanduna da ƙarafa.

Ƙungiyar ta bayyana harin a matsayin ɗaya daga cikin munanan hare-hare da aka kai kan tarukan jam’iyyun adawa tun bayan fara kamfen a watan Agusta, tana mai cewa irin wannan cin zarafi na hana ’yan siyasa da magoya bayansu amfani da ’yancinsu na yin taro cikin lumana da haɗuwa da juna.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *