Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya amince da ƙarin girma ga malamai 4,220 da sauran ma’aikatan gwamnati 3,494, bayan kammala atisayen tantance ma’aikatan da suka cancanci karin girma na shekarun 2025 da 2026.
Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin FCT, Emeka Ezeh, ne ya bayyana hakan ranar Talata, inda ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Wike na ƙarfafa gwiwar ma’aikata da inganta ƙwazon aikinsu.
Ya ce ministan ya umarci hukumar da ta biya dukkan bashin ƙarin girma da aka gada daga tsohuwar gwamnati, tare da tabbatar da cewa ma’aikatan da suka cancanta sun samu matsayinsu na gaba.
Ezeh ya kuma bayyana cewa Wike ya amince a yafe wa jami’an ilimi da suka kawo cikas ga atisayen ƙarin girma na shekarar 2025, tare da ba su damar shiga atisayen na 2026.
Bisa wannan umarni, hukumar ta gayyaci dukkan jami’an ilimin da suka cancanta domin shiga atisayen da aka kammala.
- Wike ya yi alƙawarin magance ƙarancin albashin kansilolin Abuja
-
Wike ya yi alƙawarin ba kansilan da duk ya lashe mazaɓarsa Naira miliyan 10
-
Wike ya nemi al’ummar Abuja su goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027
Shugaban hukumar ya taya waɗanda suka samu ƙarin girman murna, tare da kira gare su da sauran ma’aikata da su mayar da martani ta hanyar gudanar da ayyukansu cikin ƙwazo da kishin ƙasa.
Ya kuma sanar da cewa hukumar za ta gudanar da taron horas da ma’aikatan da ke dab da yin ritaya karo na biyu, ranar 16 ga Disamba, 2026, domin shirya su kan rayuwa bayan barin aikin gwamnati.
Ana sa ran ma’aikata 116 za su yi ritaya tsakanin 1 ga Janairu zuwa 31 ga Maris, 2027.
A watan Yulin 2026 ma, Wike ya amince da ƙarin girma ga ma’aikatan gwamnati 3,592 bayan kammala atisayen tantance waɗanda suka cancanta na shekarar 2025.