Yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, karuwar hare-hare kan ‘yan siyasa da magoya bayansu, tare da tarwatsa tarukan kamfe a wasu sassan ƙasar, na ƙara jefa fargaba kan tsaro da makomar dimokuraɗiyyar ƙasar.

Damuwa kan lamarin ya ƙaru ne bayan Majalisar Dattawa ta buƙaci rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike kan rahotannin hare-haren da aka kai kan ayarin motocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jawo ce-ce-ku-ce shi ne rahoton jifan ayarin motocin Shugaba Tinubu da wasu matasa suka yi a ranar 13 ga Nuwamba, jim kaɗan bayan ya idar da sallar Juma’a a Masallacin Shehu Shagari da ke Garki, Abuja.

Wani lamari makamancin haka ya faru a ranar 15 ga Nuwamba a ƙaramar hukumar Bichi ta jihar Kano, inda aka samu rikici tsakanin magoya bayan APC da NDC a lokacin wani rangadin siyasa.

Rikicin ya shafi ayarin motocin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce rikicin ya yi sanadin jikkatar mutane biyar da lalata motoci 13, tare da kama mutum takwas da ake zargi da hannu a lamarin. Sai dai har yanzu ana gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da yadda rikicin ya samo asali da waɗanda ke da alhakin haddasa shi.

Haka kuma, a farkon watan Nuwamba, an kai hari kan ayarin motocin Peter Obi a Calabar, babban birnin jihar Cross River, yayin da yake gudanar da harkokin siyasa. Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama wani mutum guda bisa zargin hannu a harin, yayin da ake ci gaba da bincike.

A ranar 7 ga Nuwamba kuma, an samu rikici a wani tattakin siyasa da magoya bayan NDC da Obidient Movement suka gudanar a Asaba, babban birnin jihar Delta, wanda rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar mutum guda da jikkatar wasu biyar.

Haka zalika, an kai wa ayarin motocin Atiku Abubakar hari a yankin Argungu dake Birnin Kebbi, a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.

A wani lamari kuma, an kai hari kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, da tawagarsa a wani gidan cin abinci da ke Ado-Ekiti, jihar Ekiti, a ranar 30 ga Oktoba, 2026.

A martaninta kan karuwar waɗannan matsaloli, Majalisar Dattawa ta buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, da ta aiwatar da tanade-tanaden dokar zaɓe ta 2026, ciki har da yiwuwar hana duk wani ɗan takara da aka tabbatar yana da hannu a tashin hankalin siyasa shiga zaɓe.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, rikicin siyasa da rashin haƙuri tsakanin jam’iyyu na iya kawo cikas ga gudanar da zaɓe cikin lumana da gaskiya.

Yanzu dai hankalin jama’a ya karkata ga yadda hukumomin tsaro da INEC za su magance waɗannan matsaloli, tare da tabbatar da cewa ‘yan takara da magoya bayansu za su iya gudanar da harkokin siyasa cikin ‘yanci da tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *