Kamfanin NNPC Limited, ta shirin mata masu aiki a kamfanin (Women in NNPC — WIN), ya karrama mata 20 da suka yi fice wajen aiki da samun nasarori a matakin ƙarshe na shirin “Powered By Her” na farko.
Shirin na tsawon makonni shida ne, wanda aka tsara domin bayyana nasarorin mata a cikin kamfanin, da irin gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa ayyukansu da kuma ƙarfafa sauran mata su nemi ci gaba da muƙaman shugabanci.
Babban Daraktan Gudanarwa na NNPC Limited, Bashir Bayo Ojulari, wanda shi ne babban majiɓincin shirin WIN, ya yaba wa matan 20 da suka bayyana labaransu, tare da ƙarfafa sauran mata a kamfanin da su kasance masu ƙarfin hali, jajircewa da kuma ƙoƙarin bayar da gudummawa wajen ci gaban kamfanin.
- Tinubu ya buƙaci da a bunƙasa harkokin wasanni daga tushe
- Gwamnatin Najeriya ta haɗa kai da IBSN domin ƙarfafa tsaron iyakoki
A jawabinta na musamman, Shugabar Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Ƙasa (NUPRC), Oritsemeyiwa Eyesan, ta yi kira da a ƙara ba mata damar bayyana ƙwarewarsu da samun muƙaman shugabanci.
Ta kuma yaba wa babban daraktan NNPC bisa jagorantar shirin da kuma samar da yanayin aiki da mata za su iya bunƙasa.
Taron ya haɗa mata shugabanni da ƙwararru daga sassa daban-daban na masana’antar mai da iskar gas, inda aka yi bikin nasarori, jajircewa da shugabanci, tare da jaddada muhimmancin samar da damarmaki ga mata masu tasowa a fannin makamashi.
